Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto jakadan kasar Iran a MDD yana fada a wani rahoton da ya mikawa kwamitin tsaro na majalisar a jiya Talatan.
Rahoton ya kara da cewa Sanata Lindsey Graham ya fadi wadannan maganganu ne a lokacinda ya kai ziyara zuwa HKI a cikin watan fabrairun da ya gabata. Inda yake cewa: Isra’ila ba zata tabbata ba mutukar Iran tana da shirin makamashin Nukliya, don haka, ya bukaci Isra’ila ta yi abinda ya dace, na ci gaba da kauda masana fasahar nukliyar kasar Iran.
Jakadan ya kara da cewa wannan wani furuci ne na ingiza ayyukan ta’addanci wanda Graham da wasu ‘yan majalisar dokokin kasar Amurka suke yi.
Banda haka sanatan yay i wannan maganar ne a dai dai lokacinda ake tattaunawa tsakanin kasashen 5+1 da kuma kasar Iran kan farfado yerjejeniyar JCPOA ta shirin nukiliyar kasar Iran a birnin Vienna na kasar Autria.
342/